20 Maris 2016 - 11:02
Shugaba Obama na Amurka na Ziyara a Cuba

Shugaban Amirka Barack Obama na kasar Cuba yau a wata ziyara mai dimbin tarihi, wanda ke jaddada kawo karshen zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu na tsawon shekaru 50.

Shugaba Obama da matarsa da ‘ya’yansu biyu na wannan ziyara ne na kwanaki ukuYa kasance karo na farko da shugaban kasar Amirka mai ci ke ziyara Cuba tun bayan da mayakan tsohon shugaba Fiedel Castro suka kwace mulki daga hannun Fulgencio Batista

Wannan ziyara itace karo na farko tun ziyarar Shugaba Calvin Coolidge shekaru 88 da suka gabata.288